1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Barazanar yadawar cutar Ebola a Kwango

Suleiman Babayo
August 14, 2018

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin samun yaduwar cutar Ebola saboda tashe-tashen hankula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/33AR3
Kongo Behandlungszentrum Ebola in Bikoro
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa rikice-rikicen da ake samu a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na dakile matakan yaki da cutar Ebola. Babban jami'in hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva na Switzerland cewa muddin aka gaza tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a gabashin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango akwai yiwuwar hakan zai tabarbara shirin yaki da cutar ta Ebola.

A wannan Talatar hukumomin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun tabbatar da cewa a karon farko an sami bullar cutar a wajen Lardin Arewacin Kivu. Ita dai hukumar lafiyar ta nuna muhimmanci hada kai da bangarori daban-daban domin tabbatar da yaki da cutar ta Ebola.