Rigingimu na kara ta′azzara a Burundi | Siyasa | DW | 03.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rigingimu na kara ta'azzara a Burundi

A yanzu haka dai zaman dar-dar sai karuwa yake yi a wannan kasa, inda aka gaza shawo kan tarzomar da ta barke a kan batun ta-zarcen shugaban kasar.

Walwala na neman gagaran 'yan kasar, wannan kuwa ya sa masu kananan masana'antu sun fara ji a jika, sakamakon matsalolin tsaro.

A lokacin da babu tashin hankali a kasar Burundi gidajen shaye-shaye ko na wasanni na cika ne makil da jama'a musamman ma da yammaci har ya zuwa can cikin dare a Bujumbura babban birnin kasar da ma sauran jihohi.

Sai dai yanzu bisa wannan matsala ta tashe-tashen hankulla, gidajen shaye-shayen ko na wasanni na fuskantar hare-haren 'yan bindiga, ko kuma binciken jami'an tsaro na 'yan sanda. "Wats up" wani gidan shaye-shaye ne da ya taba fuskantar hari da gurneti a 'yan kwanakin baya-bayannan a tsakiyar birnin Bujumbura. Kuma mai kula da wannan gida ya nuna damuwarsa kan iri-irin wannan akida ta kai hare-hare, domin illar hakan ita ce ta rishin cinikayya.

Burundi Pierre Nkurunziza

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi

"Da farko dai a nan ana iya saida katan-katan har goma na kayan shaye-shaye kamar su Amstel, su Primus, ko Limonade. Ammam yanzu muna saidai musali katan daya ko biyu kawai na wadannan kayan shaye-shaye. Kuma musali katan daya na Limonade sai ya yi a kalla kwanaki biyu zuwa hudu kafin mu sayar da shi abun da ya sanya a halin yanzu muka rage ma'aikata domin kusan komai ni ke gudanarwa."

A wani abun da ba'a saba gani ba mutane na komawa gidajansu da gaggawa ba kamar yadda aka saba ba, domin mafi yawa suna zowa ne su saye domin su je su sha kayansu a gida cikin iyallansu maimakon a mashaya. Wannan faduwar cinikayya da ke fuskanta a gidajan wasanni ko mashaya daban-daban ya shafi har manyan 'yan kasuwa daga koli, wadanda suke da manya-manyan shaguna ajiye kayayaki irin su barasa da sauran lemu na shaye-shaye domin suna fuskantar babban karancin ciniki. A cewar shugaban babban shagon ajiye kayayakin shaye-shayen na Ngagara tilas ce ta san ya yake ci gaba da wannan aiki a halin yanzu domin babu ciniki.

"A yau muna kokarin sayarwa amma kuma bama iya saida abun da muka saba sayarwa a baya. A halin yanzu dai muna kokarin kaiwa kostomomin mu kayayaki amma suma suna fuskantar karancin na ciniki da wajan kashi 60 cikin 100 kan yadda muka saba ciniki a baya. Amma yanzu kawai muna kokarin jurewa ne, kuma dole mu zauna mu yi jira har lokacin da masaya za su zo".

Manyan 'yan kasuwan dai, da ma wadanda suke daukan kayayaki daga garesu, na cikin tsaka mai wuya kan wannan matsala ta tsaro da ta jefasu cikin wannan mawuyacin hali na kasuwanci matsalar kuma da ke shafar har rayuwar iyallansu.

Sauti da bidiyo akan labarin