Rice da Abbas sun rattaba hannu kan taimakon tsaro a yankin Palasdinawa | Labarai | DW | 02.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rice da Abbas sun rattaba hannu kan taimakon tsaro a yankin Palasdinawa

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleez Rice sun rattaba hannu akan wani shiri na bada taimakon dala miliyan 80 domin karfafa rundunonin tsaro na Abbas.Rice tace kasar israila a shirye take ta tattauna batutuwa masu muhimmanci game da batun kafa kasar Palasdinu,bayan tattaunawarta da Abbas da kuma ministar harkokin wajen Israila Tzipi Livni.

A lokacin ziyarar tata ta kwanaki hudu a yankin gabas ta tsakiya,Rice tana kokari ne ta yada shirin Bush na gudanar da wani babban taron zaman lafiya nan gaba cikin wannan shekara.