1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Red Cross ta yi gargaɗi a kan Ebola

November 17, 2014

Jami'an Ƙungiyar Red Cross da ke taimaka wa wajen yaƙi da annobar ƙwayar cutar Ebola mai saurin kisa da ta addabi yankin yammacin Afirka sun yi gargaɗin cewar cutar na ci gaba da yaɗuwa.

https://p.dw.com/p/1Dosz
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Jami'an Ƙungiyar ta Red Cross sun bayyana hakan ne a birnin Brussels, inda suka ce a yanzu suna fuskantar babban Ƙalubale wajen Ɗaukar ma'aikatan jinya da za su tura yankin yammacin Afirka da ke fama da annobar ta Ebola. A yayin da yake jawabi jami'i a Ƙungiyar Red Croos ta ƙasar Faransa Antoine Petitbon ya ce sun ɗauki ma'aikata da dama da suka nuna aniyarsu ta zuwa yankin yammacin Afirka, waɗanda daga baya suka janye sakamakon matsin lamba daga iyalansu da kuma abokan arziki na fargabar kada su je su kamu da cutar ta Ebola.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane