1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Red Cross ta tsaida aiki a Afganistan

Abdul-raheem Hassan
April 11, 2019

Kungiyar ta ce matakin dakatar da aiki a Afganistan ya biyo bayan rashin tabbacin tsaro da zai ba ta damar gudanar da ayyukanta a sassan kasar da mafi yawa ke karkashin ikon mayakan Taliban.

https://p.dw.com/p/3GdWc
Symbolfoto Internationale Rotkreuz- und Rothalbmond-Bewegung
Hoto: Getty Images/C. Sung-Jun

Matakin kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross na zuwa ne bayan barazanar da kungiyar Taliban ta sanar na haramta ayyukan kungiyoyin agaji na Red Cross da hukumar lafiya ta duniya a Afganistan.

Taliban ta zargi kungiyoyin da saba yarjejeniyar aiki a yankunansu tare da tuhumar hukumar lafiya ta duniya da leken asiri yayin gudanar da gangamin rigakafi.

Kawo yanzu babu martani daga bangaren WHO kan wannan mataki da Taliban ta dauka, sai dai akwai fargaba matakin zai shafi dubban mutanen karkara da ke fama da cutar shan inna.

Kasashen Afganistan da Pakistan da Najeriya na cikin kasashen da ake yawan samun bullar cutar polio akai akai duk da cewa alkaluma na nuna raguwar cutar da kashi 99 tun shekarar 1988.