1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Real Madrid ta lashe Champions League karo na 15

June 2, 2024

Kungiyar kwallon kafar Spain ta Real Madrid ta lashe gasar zakarun turai da ake wa lakabi da Champions League.

https://p.dw.com/p/4gXbJ
Hoto: Carl Recine/REUTERS

A karawar karshe da ta yi a ranar Asabar da daddare da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmundta Jamus a filin wasa na Wembley, Real Madrid ta lallasa Jamusawan da ci 2-0.

Godiya ga mai tsaron baya na Real Madrid Dani Carvajal wanda shi ne ya yi kukan kura ya fara zura wa Dortmund kwallon farko a mintuna na 74 yayin da dan wasa Vinicius Junior shi ma ya gwada sa'arsa ya zura wa kungiyar kwallon kafar Jamus din kwallo ta biyu a yayin da ake mintuna 83 da fara wasan

Wannan shi ne karo na 15 ke nan da kulob din na Real Madrid ke lashe gasar ta Champions League, matakin da tun da aka kafa gasar wata kungiya ba ta taba samunsa ba.

Tun da farko hukumomi sun samar da jami'ai sama da 2,500 da aka girke a sassa dabam-dabam na filin wasan na Wembley domin hana barkewar yamutsi irin wanda aka samu lokacin wasan karshe na gasar Euro 2020, inda 'yan kallo da ba su da tikiti suka shigo fili suka haifar da rudani.