Rayuwar ′yan gudun hijira a Najeriya | Siyasa | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rayuwar 'yan gudun hijira a Najeriya

'Yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya na neman ɗauki a cikin wannan wata na azumin Ramadan

Alltagsleben im Flüchtlings-Camp Malkohi, Nigeria

Sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi, a Najeriya

Barazanar hare-hare na mayaƙan Ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu baya ga dubban da suka mutu a garuruwa daban-daban na wannan shiya.Wasu daga cikinsu masu yawa sun sami mafaka a Yola fadar jihar Adamawa.

'Yan gudun hijirarna buƙatar samun agaji a cikin wannan wata na azumi

Alltagsleben im Flüchtlings-Camp Malkohi, Nigeria

Sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi, a Najeriya

Yayin kuma da al'ummar musulmin duniya suka fara yin azumin ,musulmai daga cikin waɗanda suka gujewa rikicin na Boko Haram na buƙatar samun ingacin rayuwa don ba su damar yin azumi a yanayi mai ɗan sauƙi kamar sauran al'umma. malam Abubakar Isa, ɗaya daga cikin 'yan gudun hijirar da suka soma azumin a sansanin Malkohi da ke yankin ƙaramar hukumar mulki ta Yola ta kudu, da ke a fadar jiha ya ce suna cikin wani hali na buƙata. Itama wata mai sunan malama Hauwa, ta ce lokacin na azumin kamar yadda kowa ya sani akwai buƙatar a inganta abinci da kuma yanayi na ibada a wannan lokacin da musulmin ke ribibin neman lada saboda yawan falala da ke cikin watan na azumi.

Kiraye-kiraye daga jama'a domin taimaka wa 'yan gudun hijirar

Screenshot Alltagsleben im Flüchtlings-Camp Malkohi, Nigeria

Sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi, a Najeriya

Tuni dai malamai suka soma kiraye-kirayen jama'a kan buƙatar taimaka wa waɗannan mutanen da ke cikinwani hali rayuwa marasa kyau,waɗanda suke ganin ya zama wajibi masu hannu da shuni da kuma gwamnati ta yi wani yunƙuri na musammun domin taimaka wa waɗannan mutanen.

Sauti da bidiyo akan labarin