Rayuwar anguwar matalautan Namibiya | Himma dai Matasa | DW | 02.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Rayuwar anguwar matalautan Namibiya

A harshen Otjiherero da ke kasar Namibia, Katutura na nufin "Wurin da mutane ke kyamar zama", wanda anguwa ce a gefen Windhock babban birnin kasar da ya fuskanci banbanci alokaci mulkin wariyar launin fata.

A wannan anguwar dai bakaken fata ne kadai ke zama, samun ruwa a anguwar ya zama kamar wani abun kawa, talauci da yawaitar ciwo mai karya garkuwar jiki wato HIV-AIDS da tashe -tashen hankula sun yi wa anguwar katutu.

Samauel Kapepo na daya daga cikin wadanda suka yi rayuwa a anguwar Katutura, ya rasa iyayensa sakamakon ciwon HIV. A lokacin da ya ke saurayi ya kasance yana daukar dawainiyar kansa, ya fuskanci mummunan kalubale daban daban a rayuwarsa, amma ya cigaba da gudanar da rayuwarsa a hankali. A yanzu cikin sa´a yana jagorantar wani shiri na ciyar da kananan yara kusan 500, sau biyu a mako wadanda ke gararamba kan tituna, bisa rashin galihu.

Samuel Kapepo ya ce dukkannin gararambar da yara ke yi bakin tituna a garinsa ba bakon abu bane, kusan ma ya bayyana cewa zai iya zama daya daga cikinsu, ganin ya rasa iyayensa tin yana dan shekara 13, inda ya kara da cewa.

"Na taso cikin gurbataccen yanayi, ni dai kam rayuwa bata yi min kyau ba. Na tashi babu iyaye, babu abinci kuma babu ingantaccen ilimi, saboda duk abunda ka gani ina baiwa kaina kwarin gwiwa ne, ganin irin kalubalen da na fuskanta. Naga ya kamata in tashi tsaye in yi aiki tukuru in bada gudumawa ta, wani lokacin na kan shiga cikin aljihu na, in bada don taimakon yaran, su samu abinda za su ci"Mafi yawancin wadannan yaran ko dai iyayensu sun watsar da su, ko kuma marayu ne, kamar yadda Samuel ya bada misali da kansa. Ya ce Namibiya dai karamar kasa ce, wadda kusan kashi talatin cikin dari na al'ummar kasar 'yan kasa da shekaru14. Amma a kididdigar kwana kwanannan da aka gudanar a kasar ta Namibiya, ta nuna cewa akwai akalla marayu 140,000. Rabi daga cikinsu an barsu ne sakamakon iyayensu sun rasu ta hanyar cutar HIV. Yaran da suka rasa iyayensu ta wannan hanyar mafi lokuta sukan rasa yan uwa wadanda zasu dauki nauyinsu, inda ya kara da cewa.

"Yawancin yaran an haifesu da cutar HIV, wasu daga cikin iyayensu sun rasu sakamakon cutar, wasu kuma iyayen basa iya gudanar da aiki saboda cutar. Cutar HIV a kasar Namibiya ta taimaka wajen kara babbar rata kwarai da gaske"

A yanzu dai Samuel Kapepo ya zama jarumin gaske a kasar ta Namebiya mai fada aji, ya kuma yi nasara wajen gina kekkyawar ma'amala tsakanin masu gararamba, ta yadda za su zamo masu dai-dai a al'amuran yau da kullum a kasar. A yanzu kuma ya kammala shiri tsab dan jagorantar sauran marasa galihu.

Sauti da bidiyo akan labarin