Rayuka sun salwanta a harin kunar bakin wake a Maiduguri | Labarai | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rayuka sun salwanta a harin kunar bakin wake a Maiduguri

A cewar shelkwatar jami'an sojan kasar ta Najeriya da ke Abuja, mutane 14 ne suka rasu a cikin harin ciki kuwa har da 'yan bindigar.

Nigeria - Maiduguri

Mutane a wurin da aka kai farmaki

Sama da mutane 10 ne suka rasu yayin da wasu 39 suka samu raunika bayan da wasu 'yan kunar bakin wake hudu suka kai farmaki a birnin Maiduguiri fadar gwamnatin jihar Borno kamar yadda jami'an sojan Najeriyar suka bayyana a ranar Juma'an nan.

A cewar shelkwatar jami'an sojan kasar ta Najeriya da ke Abuja, mutane 14 ne suka rasu a cikin harin ciki kuwa har da 'yan bindigar sannan 39 suka samu raunika a harin na cikin daren Alhamis.

Sanarwar jami'an ta kara da cewa 'yan bindigar guda uku sun tashi jigidar bam da ke jikinsu yayin da guda dayan kuma ya tashi nasa bam din a gaban masallaci.

Tun bayan da mayakan na Boko Haram suke fiskantar barin wuta daga dakarun sojan kasar da na kasashe makwabtan Najeriya yanzu sun mike da kai hare-hare irin na sari ka noke da ke karewa mafi akasari kan fararen hula.