Rawar gidajen sauro a yaki da cutar Maleriya a duniya | Siyasa | DW | 25.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rawar gidajen sauro a yaki da cutar Maleriya a duniya

Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa cutar zazzabin cizon saura na hallaka mutane a kalla dubu 400 kowace shekara.

Ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara rana ce da duniya ke yin bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro wanda aka fi sani da Maleriya da nufin yin duba kan nasarori ko akasin haka da a kokarin yakar barnar da cutar ke yi musamman a kasashen 'yan rabbana ka wadata mu.Taken bukin na bana dai shi ne kawo karshen cutar Maleriya saboda amfanin al'umma.


Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa cutar zazzabin cizon saura na hallaka mutane a kalla dubu 400 kowace shekara abin da ya sa ta tashi haikan domin rage irin barnar da cutar ke yi musamman a kasashen masu tasowa.


Matakai da hukumomi ke dauka ya haifar da alherin da ake nema inda tun a shekara ta 2000 ake samun raguwar barnar da cutar ke yi a kusan dukkanin nahiyoyin duniya. Ana alakanta samun nasarar yaki da cutar zazzabin cizon sauro da yadda gwamnatoci a kasashen ke bada tallafi da kungoyoyin agaji na duniya suka yi aikin raba gidajen sauro masu dauke magunguna tare da gudumowar shugabannin addini da na al'umma.


Sai dai matakai da ake dauka ba su wadaci sansanonin 'yan gudun hijira ba wanda yawancin ke zaune a wurare marassa tsabta inda ake samun karuwar masu fama da cutar.


Dr. Sale Abba wani likita ne da ke aikin agaji a sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri ya ce yawancin wadan da suke zuwa wajensu da maganar rashin lafiya binciken su na nuna musu cewa zazzabin cizon sauro ne.


Masu yaki da cutar zazzabin cizon sauro sun nemi rubanya kokarin da ake don yaki da cutar a sansanonin 'yan gudunn hijira musamman ganin a fuskantar damuna inda kuma suka shawarcin 'yan gudun hijira su ke tsabtace muhallansu tare da tabbatar da amfani da gidajen sauro ga wadan su suka samu.

Sauti da bidiyo akan labarin