Maleriya cuta ce ta zazzabin cizon sauro wanda ake samu galibi a kasashen kudu da Sahara na Afirka, kuma wadda take kan gaba wajen kashe mutane.
Kasashen duniya sun tashi tsaye wajen ganin sun magance cutar, kuma ana samun nasara, amma akwai gagarumin kalubale har yanzu musamman tsakanin kasashen Afirka na kudu da Sahara.