1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zabe a kasar Libiya

Mahmud Yaya Azare SB/LMJ
June 8, 2023

Bayan kwashe kwanaki 10 suna tafka zazzafar muhawara, wakilan kwamitin da ke shirya zaben Libiya, sun sanar da cimma matsaya kan dokokin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/4SLT9
Schweiz Libysches Dialogforum in Genf
Taron tattauna batun LibiyaHoto: UNITED NATIONS/AFP

A wata ganawa da manema labarai a birnin Bouzniga na kasar Moroko, da kwamatin hadin guiwar kwar shida na bangarori masu rikici a Libiya da aka doramar alhakin  tsara jadawali da dokokin zaben kasar ya yi, shugaban tawagar kwamitin, Jalal Al-Shuwaidi, wanda ya mika godiyarsa ga Masarautar Moroko bisa karbar bakuncin tarukan kwamitin a cikin kwanaki goma da suka gabata, da kuma godiya ga kokarin da take yi na tallafawa kasar Libya. ya bayyana cewa, sun kammala tsara dokokin zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar, ba tare da sun fuskanci matsin lamba ko tsoma baki daga Maroko ko kuma daga wasu kasashen ketare ba, lamarin da zai kawo karshen doguwar dambaruwar siyasar da kasar ta tsunduma tun bayan kifar da Marigayi Muammar Gaddafi shekaru 12 da suka gabata:

Schweiz Libysches Dialogforum in Genf
Tattauna batun LibiyaHoto: UNITED NATIONS/AFP

Batun hana masu dauke da shaidar zama yan kasashe biyu da mukarraban kanal Gaddafi gami da bawa sojojin da suka cire kakai suka tsaya takara damar sake mayaar da kakakinsu idan suka fadi a zabe,sune manyan batutuwan da sukai ta jawo ta da jijiyoyin wuya a yayin tattauna dokar zaben,lamarin da kwamatin ya cimma matsaya kansa,duk da cewa,yayi ammanar zata iya fuskantar adawa majalisun,muddin kowane bangare bai sauko daga  hawa kujeran naki ba, inji shugaban tawagar bangaren zartaswa a kwamitin Omar Boulifa.

A mako mai zuwa ne dai majalisun biyu na Libiya za su yi zaman rattaba hannu kan amincewa da daftarin dokar zaben.To sai dai tun kafin aje ko'ina, murna ta fara komawa ciki ga 'yan kasar da ke cike da fatan kawo karshen dambaruwar siyasa da matsalolin tsaron da suka addabi kasar, saboda ficewa daga zauren taron na birnin Bouzniga da shugaban majalisar dokokin kasar Aqilah Saleh da shugaban majalisar dattijai, Khaleed Mushry suka yi, tun kafin a kammala taron.