Rashin zaman lafiya a Mali da zaben kasar Guinea | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Rashin zaman lafiya a Mali da zaben kasar Guinea

Halin rashin tabbas a Mali da fargabar barkewar rikici bayan zabe a Guinea da rashin sanin makomar shirin zabe a Kwago sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

Symbolbild - Minusma Mali

Dakarun Minusma a Mali

Za mu fara sharhin jaridun a Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a wannan mako ta leka kasar Mali.

Ta ce har yanzu babu kwanciyar hankali a kasar Mali tun bayan da gwamnati da masu kishin addini da kuma Abzinawa suka fara fada da juna. Ta ce duk da cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya amma ba dukkan bangarorin da ke fada da junan ne ke aiki da ita ba. A cikin watan Maris na shekarar 2012 rikicin da aka dauki shekaru gommai ana yi tsakanin 'yan tawayen Abzinawa da gwamnatin Mali ya rincabe kuma tun daga lokacin har yanzu kasar ba ta ga wani zaman lafiya mai dorewa ba, duk da kai komo da kasashen duniya suka yi ta yi na yin sulhu hade da girke dakarun duniya a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Zabe a wata kasa da cin hanci ya yi wa katutu

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sharhi ta yi game da zaben kasar Guinea tana mai cewa shugaban kasa Alpha Conde ya kama hanyar lashe zaben 'yan majalisar dokoki.

Guinea Wahl 2013 Alpha Conde

Shugaba Alpha Conde ya doshi hanyar lashe zabe

Ta ce sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta Guinea ta tattara na kimanin kashi 25 cikin 100 daga kuri'u miliyan shida da aka kada, sun nuna shugaba Conde ne ke kan gaba da fiye da kashi 50 cikin 100. Sai dai a ranar Alhamis babban mai kalubalantarsa Cellou Dalein Diallo ya ce ba zai amince da sakamakon ba, kuma ya janye daga takarar neman shugabancin kasar. Diallo dai ya yi zargin tabka magudi a zaben. Amma a nasu bangaren masu sanya ido kan zabe na kasashen tarayyar Turai sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Tosai dai sun nuna rashin gamsuwa da shirye-shiryen da hukumar zaben ta yi. Ana fargabar barkewar tashin hankali bayan an sanar da sakamakon zaben a hukumance a karshen wannan mako.

Kabila na rasa abokanen dasawarsa

Daga batun siyasar Guinea Konakry sai na wani rikicin kuma a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango inda jaridar Die Tageszeitung ta labarto cewa shugaba Kabila na rasa abokan dasawarsa.

Joseph Kabila Kabange

Joseph Kabila Kabange na Kwango

Ta ce a kullum abokan dasawar Shugaban Kwango Joseph Kabila na juya masa baya. Na baya bayan nan shi ne shugaban hukumar zabe Labbe Appolinaire Malumalu wanda ya yi murabus. Jaridar ta ce yanzu haka dai ba ma wanda ya yi amanna cewa za a gudanar da zabukan 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa a shekarar 2016 kamar yadda aka tsara. Hakazalika babu wanda ya san makomar kasar da kuma shi kanshi shugaban kasa. Tuni dai Majalisar dinkin Duniya ta yi gargadi game da akuwar wan rikici.

Cututtuka bayan waraka daga Ebola

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta buga labari game da abin da ta kira radadi bayan wata annoba.

Ta ce dubun dubatan mutane sun samu waraka daga cutar Ebola, amma tabbas kwayoyin cutar ka iya boya a cikin jikin dan Adam, inda garkuwar jikin dan Adam ba ta iya cimma musu. Wadannan wurare na jikin dan Adam sun hada da cikin ido da kwakwalwa da kwan mace da mahaifa da nono da kuma wasu gabobi na jikin dan Adam. Jaridar ta kara da cewa a yankin yammacin Afirka an saba samun masu fama da wasu cututtuka bayan sun warke daga cutar Ebola, inda wasu ke fama da larura ta makanta wasu kuma kan shiga tsananin damuwa. Saboda haka akwai bukatar ci gaba da tallafa wa mutanen da suka warke da Ebola don kawo musu saukin wannan radadi.