1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin wutar lantarki a Afirka ta Kudu

October 4, 2022

Wasu 'yan kasashen waje da ke harkokin kasuwanci a Afirka ta Kudu, na kokawa kan rashin sanin tabbas game da makomarsu sakamakon matsalar yawan daukewar wutar lantarki da ake fuskanta

https://p.dw.com/p/4HjoL
Matsalar wutar lantarki ta yi kamari a Afirka ta Kudu
Matsalar wutar lantarki ta yi kamari a Afirka ta KuduHoto: Shafiek Tassiem/Reuters

Sabanin 'yan asalin kasar Afirka ta Kudu wadanda ake iya cewa cikin kasarsu suke, bakin da ke shiga kasar daga wasu yankuna na Afirka na dogaro da wasu ayyuka na kashin kai da yawanci kan kasance kananan ayyuka.

Galibi dai na aiki ne a gidajen sayar da abinci da wasu ma'aikatun da suka dogara da wutar lantarki. Yayin da wasu yankuan ke zama babu wutar na tsawon akalla sa'o'i tara a kullum, bakin da ke sana'ar aski da kwalliyar mata da sayar da abinci da ma walda, na ci gaba da zama babu abin yi da zarar babu wuta.

Afrika ta Kudu,  Tattalin arziki da rashin wutar lantarki
Afrika ta Kudu, Tattalin arziki da rashin wutar lantarkiHoto: Reuters/S . Sibeko

Wasu daga cikin su da kan samu kudade ne da yammaci lokacin hada-hadar bayan maraice, ba su da wani zabi face gaggauta komawa gida saboda gudun gamuwa da 'yan kwace. Wani Debo Adesina, shi ne shugaban wata kungiya mai kare muradun 'yan Najeriya da ake kira Nigerian Lives Matter, wanda ke kokawa kan halin da suke a ciki.
"Duk wata hada-hadar kasuwanci da mutane ke yi a Afirka ta Kudu a yanzu na komawa baya. Mutanenmu na kuka. Kananan harkokin da aka saba yi sai tsayawa suke ta yi. Sannan ga kyashi da kyama da suke fuskanta, duk sun hadu sun dagula lamura".

Haka labarin yake ga su ma 'yan kasashen Somaliya da Habasha da ke a Afirka ta Kudu, inda shugabansu Amir Sheikh, ya ce kama daga fashi da masu fasa shaguna duk sun karu saboda duhun rashin wuta. Wani abun kuma shi ne ba su da inshora kan kayayyakinsu, don haka wadanda ke lalacewa na ta lalacewa babu yadda za a iya mayar da gurbinsu ko rage asara, sai kuma babban abun maganar rage ma’aikata da ma rufe harkoki da ke karuwa.

Afirka ta Kudu | Farantan Sola, Samar da wutar lantarki da hasken rana
Afirka ta Kudu | Samar da wutar lantarki da hasken ranaHoto: Schalk van Zuydam/AP Photo/picture alliance

Su ma mata wadanda ke shiga Afirka ta Kudun domin nema, a cewar Victress Mathuthu, shugabar kungiyar matan Zimbabwe abun babu dadi.
Mata da dama ne ake da su da ke ayyyukan gyaran gashi da kwalliya, da gidajen sayar da abinci da na shan barasa da ma sauran harkoki na kan tituna. Wanda batu na karancin wuta na yi wa mutane illa. Akwai yiwuwar mu sake shiga yanayi na rufe harkokin samun kudade 

Kamfanin da ke samar da wutar lantarki a Afirka ta Kudu wato Eskom, ya danganta katsewar wutar da lalacewar wasu na'urori da kuma gyare-gyaren da ake yi daga lokaci zuwa lokaci, sai kuma ya baiyana karuwar masu bukatar wutar kusan kullum, a matsayin manyan dalilan da ke haddasa daukewar ta.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi kira ga al'umomi su kara hakuri saboda halin da aka shiga, hasali ma yace ba matsala ce da za ta kau cikin kankanin lokaci ba, amma kuma ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta shawo kan lamarin. 

Kwararru dai na gargadi kan illar da karancin wutar za ta haifa wa tattalin arzikin Afirka ta Kudu, ganin yadda dubban mutane ke rasa ayyukan yi))