Rashin tabbas game da zaman sulhun Siriya | Labarai | DW | 08.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin tabbas game da zaman sulhun Siriya

Kungiyar 'yan tawayen Siriya ta dage kuri'ar da ta shirya kadawa dangane da hallarta ko akasin haka na taron zaman sulhu game da rikicin kasar wanda za a yi a kasar Switzerland.

default

Shugaba Bashar al-Assad na Siriya

Kungiyar ta Syrian National Council ta ce ta dau wannan mataki ne saboda rikicin cikin gida da ta ke fuskanta, lamarin da ya sanya ake cigaba da nuna shakku na yiwuwar tattaunawar.

Guda daga cikin jiga-jigan 'yan tawayen Hadi Al Bahra ya ce akwai yiwuwar su gudanar da wannan zabe da zai bayyana matsayin kungiyar game da halartar taron ranar sha biyar ga wannan watan.

Tuni dai aka fara danganta wannan tsaiko na bayyana matsayin 'yan tawayen na shiga tataunawar da yiwuwar da ake da ita ta shigar Iran wadda gwamnatinta ke dasawa da shugaba Bashar al-Assad cikin jerin kasashen da za su hallarci ganawar ta Geneva.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu