1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas a dangantakar Larabawa da kasashen Turai

Abdullahi Tanko Bala
February 26, 2019

Ga dukkan alamu har yanzu tana kasa tana dabo a dangantaka tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Larabawa. Kasashen dai sun gana a Masar.

https://p.dw.com/p/3E7Xm
Ägypten Sharm el Sheikh Gipfel von EU und Arabische Liga
Manyan jagoroin kasashen Turai da na Larabawa a taron kasar MasarHoto: Getty Images/D. Kitwood

A wannan sharhi da Bernd Riegert ya rubuta, ya ce yankunan biyu suna da sabani babba kamar yadda muradunsu suka rarraba.

Bernd Riegert ya fara da tambayar shin taron kolin da ya gudana tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da kasashen Larabawa holoko ne kawai babu wani abu a cikinsa ko taron shan shayi? 

Ya ce a fakaice kusan haka abin yake saboda babu wasu shawarwari ko matakai kwarara da aka gani a jadawalin taron na farko tsakanin kungiyar tarayyar Turai da kasashen Larabawa. To amma babu wanda ya tsammaci haka.

Scharm el Scheich Gipfel der EU und der Arabischen Liga
Hoto: Reuters/M. El Ghany

Babban makasudi haduwar ta farko shi ne ganawa da juna da kuma shata jadawalin tattaunawa a gaba. An yi ganawar ta diflomasiyya a Sharm el Sheikh, sai dai kuma ta gudana ne ba tare da samun karsashi da aka yi fatan gani da zai kai ga cimma burin kudirorin da aka sanya a gaba ba.

 

Sai dai kuma duk da haka an duba muhimman batutuwan yakin basasa da suke ciwa kasashen Siriya da Yemen tuwo a kwarya. An kuma bada shawarwari kan yadda za a samar da daidaito da kwanciyar hankali a kasr Libya.

Amma ba hurumin kungiyar Tarayyar Turai ba ne ko kawancen kungiyar kasashen Larabawa da ba ta da karfin tasiri ta iya aiwatar da wani abu.

Ägypten Gipfel EU und Arabische Liga in Sharm El Sheikh Merkel und al-Sisi
Angela Merkel da Shugaba al-Sisi na MasarHoto: Imago/Xinhua/A. Gomaa

Kasar Masar wadda ta karbi bakuncin taron ta fayyace cewa bata aminta da shawarar kungiyar tarayyar Turai ba na yin sansanin dakatar da yan cirani daga Afirka na tsawon lokaci ba a kasar. Wannan batu dai ya fayyace yadda bangarorin biyu na Kungiyar tarayyar Turai da kuma kasashen Larabawa ke bukatar juna.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ma kara da baiyana wannan mataki da cewa yana da muhimmanci ga dorewar makomar kungiyar Tarayyar Turai.