1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara sun wa makarantu kaura a Kamaru

Fatima Ibrahim Mu'azzam YB
September 4, 2018

A Jamhuriyar Kamaru a daidai lokacin da ake komawa sabon zangon karatu na shekara ta 2018, dubban yaran makaranta ne na yanki masu magana da turancin Ingilishi ba su hallara a makarantu ba, saboda fargabar tsaro.

https://p.dw.com/p/34Geb
Kamerun Muttersprachenunterricht
Hoto: DW/H. Fischer

Bayan watanni hudu na hutu ne 'yan makarantar firamare da sakandire suka koma makaranta a Kamaru, a cikin yanayi na rashin tabbas a yankunan arewa da ke fama da rikicin Boko Haram da kuma yankin masu magana da harshen Ingilishi da ke fama da rikicin aware a arewacin kasar.

Kamerun Kinder im Dorf Mboh
Hoto: DW/H. Fischer

Mbuh Emmanuel shi ne babban malamin makarantar firamaren gwamnati da ke garin Mbengwi, bai samu yaro ko daya ba a makarantarsa abin da ya ba shi damar zuwa kasuwanni da fada-fada domin shawo kan iyayen yaran dan su bar yaransu su koma makaranta.

Wasu iyayen kamar Mua Patrick sun bayyana cewar ba za su amsa wannan gayyatar ba saboda ba su da tabbacin tsaron yaransu kamar yadda Mua ya bayyana.

Kamerun Muttersprachenunterricht
Hoto: DW/H. Fischer

 A yanzu dai kimanin makarantu 150 ne suke rufe sakamakon hare-hare ko barazana na wadannan 'yan bindiga. Bernard Okalia Bilai wanda yake zaman gwamnan yankin Kudu maso Yammacin Kamaru ya ce an kashe 'yan bindiga da dama kuma ya umarci iyaye da su daina fargabar tura yaransu makaranta saboda wadannan 'yan bindigar.

Tsarin karatu mai ruwa biyu ne dai Kamaru ke amfani da shi, inda wasu 'yan kasar ke amfanin da tsarin Ingilishi yayin da wasu ke amfani da Faransaci ba tare da la'akari da asalin yankin ba. Sai dai daga baya-bayannan gwamnatin kasar ta fitar da tsarin karatu da ke dunkule Faransanci da Ingilishi wuri guda.