Rasha ta yi na′am da tayin sulhu da ′yan adawar Siriya suka yi | Labarai | DW | 21.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta yi na'am da tayin sulhu da 'yan adawar Siriya suka yi

Rasha ta ce za ta samar da kyakkyawan yanayin kulla yarjejeniyar sulhu a tsakanin gwamnatin Siriya da 'yan adawar kasar.

Russian Foreign Minister Sergei Lavrov (L) walks with the Secretary-General of the Arab League Nabil Elaraby prior to a Russia-Arab cooperation forum in Moscow February 20, 2013. REUTERS/Pool (RUSSIA - Tags: POLITICS)

Sergei Lavrov da Nabil al-Arabi

Gwamnatin Rasha tare da kungiyar kasashen Larabawa sun bukaci gwamnatin Siriya ta amince da tayin zama kan teburin shawarar da 'yan adawar kasar suka gabatar mata, kana ta kulla yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi na kusan shekaru biyu kenan. A lokacin daya ke jawabi a wannan Larabar, sakatare janar na kungiyar kasashen Larabawa Nabil al-Arabi ya shaidawa Rasha irin nauyin daya rataya a wuyanta, na bukatar yin anfani da karfin fada-ajin da ta ke da shi akan Siriya, domin taimakawa shawo kan rigingimun da kasar ke fama da shi. Ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya bayyana cewar a shirye yake ya karbi bakuncin duk wani taron da zai gudana a tsakanin shugaba Bashar al-Assad na Siriya da kuma wakilan 'yan adawar kasar, amma ya jaddada cewar babu alamar matakin soji ne kawai zai warware rikicin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu