1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta karbe iko da yankunan Donbass

Abdourahamane Hassane
May 20, 2022

Ministan tsaron na kasar Rasha Igor Konashenkov, ya ba da tabbacin cewar sojoinsu sun kusan kammala mamaye yankin Lugansk na kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Be24
Ukraine-Krieg Mariupol | russischer Soldat
Hoto: Vladimir Gerdo/Tass/dpa/picture alliance

Ministan ya ce bayan haka sojojin na Ukraine dubu 1,908 da suke jibge a kamfanin sarrafa karafa na Azovstal da ke Mariupol suka mika wuya ga sojojin rasha ministan ya ce "Rukunin sojojin kasar Rasha tare da wasu gungun 'sojojin  na Jamhuriyar Lugansk da Donetsk na ci gaba da kara karfin iko a yankunan Donbass da suka kwace kwata-kwata. Rahotannin sun ce wani babban kwamandan soji na ukraine shi ya ba da umarnin  ga sojojin da su dakatar da kare birnin domin ceton rayuka.