1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce za ta ci gaba da dafawa Assad

January 10, 2014

Rasha ta shaidawa Amirka cewar za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya a yaki da 'yan tawaye da ke kokarin kawar da shi daga mulki.

https://p.dw.com/p/1Aota
Shugaban Siriya Bashar al-AssadHoto: Reuters

Jami'an diflomasiyyar Rasha ne suka bayyana hakan yayin wani taro da suka yi da takwarorinsu na Amirka gabannin taron da za a yi tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavarov da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry tare da manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Larabawa kan rikicin na Siriya Lakhdar Brahimi.

Rashan dai ta ce ta dau wannan matsayi ne domin kuwa gwamnatin Assad na bukatar tallafi wajen yakar 'yan tawayen da suka himmatu wajen ganin zaman lafiya ya ki wanzuwa a kasar, to sai dai ya zuwa yanzu Amirkan ba ta maida martani kan wannan matsayin na Rasha ba.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan kafin babban taro na lalubo hanyoyin warware rikcin Siriyan da za a yi a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh