Rasha ta ce lafiyar shugaba Putin kalau | Labarai | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ce lafiyar shugaba Putin kalau

Hukumomin Rasha sun karyata cewa shugaba Vladimir Putin na fama da rashin lafiya. Sai dai ba su fayyace lokacin da za a ganshi a bainin jama'a ba a kwana-kwanannan.

Fadar shugaban kasar Rasha ta mayar da martani dangane da rade-raden da ake yayatawa cewar shugaba Vladimir Putin ba shi da lafiya. Kakakin fadar mulki ta Kremlin Dmitri Peskow ya ce shugaban na Rasha na cikin koshin lafiya. Dangane da tambayar da aka yi masa a kafofin sadararwa dangane da lokacin da za a sake ganin Putin a bainin jama'a, jami'an ya yi jirwaye mai kama da wanka.

Sai dai kuma wata sanarwa da fadar ta Moscow ta fitar ta nunar da cewa shugaban na Rasha zai halarci taron cika shekaru 100 da kaddamar da kisan kare dangi na Armeniya da zai gudana a ranar 24 na watan Afirlu mai zuwa.

'Yan adawan kasar ta Rasha suna kururutawa cewar Vladimir Putin mai shekaru 62 da haihuwa na fama da matsananciyar rashin lafiya. Tun dai makon da ya gabata ne aka ga Putin a bainin jama'a a karon karshe, lokacin da ya gana da firaministan Italiya Matteo Renzi.