Rasha bata da sojoji a gabacin Ukraine | Labarai | DW | 11.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha bata da sojoji a gabacin Ukraine

Ministan harkokin waje Sergei Lavrov ya karyata zargin da gwamnatin Ukraine ke wa Rasha, na jibge jami'an tsaro a kan iyakokin kasashen biyu ta gabashi.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya karyata zargin da ake wa Moscow na jibge sojoji a kan iyakarsu da Ukraine ta gabashi, yankin da ke neman ballewa daga Kiev. Ya ce basu da jami'an tsaro a wannan yanki kamar yadda a ke zargi. Lavrov ya ce ko shakka babu akwai 'yan Rasha da ke zama a yankin, kasancewar wuri ne da ke da dumbin jama'a. Gwamnatin rikon kwaryar kasar Ukraine dai ta zargi Moscow da kasancewa ummul aba'isin boren da ke gudana a yankin gabashin kasar da suka hadar da birnin Donetsk da Lugansk, inda masu goyon bayan Rasha ke ci gaba da mamaye gine ginen gwamnati, kuma ke neman a basu 'yancin cin gashin kai.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe