Rasa rai bayan tsagaita wuta a Ukraine | Labarai | DW | 15.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasa rai bayan tsagaita wuta a Ukraine

Jami'an tsaro da fararen hula da dama ne suka rasuwa tun bayan da 'yan aware dake samun goyon bayan kasar Rasha suka kwace yankunan gabashin kasar ta Ukraine.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na ranar Litinin ya ce da yawa daga cikin mutanen da suka saura a yankin gabashin Ukraine na cikin mawuyacin halin rayuwa.Ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 12 da suka hadar da jami'an tsaro da fararen hula ne suka rasu tun bayan da 'yan aware da ke samun goyon bayan kasar Rasha suka kwace yankunan gabashin kasar ta Ukraine da ke makwabtaka da kasar Rasha.

Cikin wannan adadi na mamatan kusan kashi talatin cikin dari an sam su ne bayan shirin tsagaita wutar da aka cimma a ranar biyar ga watan Satumba. Ragowar kuwa sun rasu ne kafin wannan rana kamar yadda rahoton na nunar.