Rantsuwa ta biyar a mulkin Idriss Deby a Chadi | Labarai | DW | 08.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rantsuwa ta biyar a mulkin Idriss Deby a Chadi

'Yan adawa a kasar sun bayyana ranar rantsuwar kama aikin Shugaba Deby a karo na biyar a matsayin ranar makoki.

Tschad Präsident Idriss Deby

Shugaba Idriss Deby

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya shirya tsaf dan rantsuwar kama aiki a zangon wa'adi na biyar a ranar Litinin din nan, duk kuwa da samun turjiya da shugaban ke samu daga bangaren 'yan adawa, da suka bayyana ci gaba da wa'adinsa a matsayin kama karya.

Jami'an tsaro da kayan yaki a birnin Ndjamena sun yi nasara ta tarwatsa dandazo na 'yan fafutika da 'yan adawa a wannan kasa a karshen mako, bayan da suka fita gangamin da suka kira duk kuwa da cewa mahukunta a kasar ta Chadi sun ja musu kunne da kada su fita.

Akwai dai 'yan fafutika da dama a kasar ta Chadi da suka bayyana wannan rana ta Litinin da shugaba Deby zai sake rantsuwar kama aiki a matsayin ranar makoki, ranar da ake tsammanin baki da shugabanni daga kasashen duniya musamman na Afirka da ke kawance ta Chadi za su halarci bikin rantsuwar.