Rajoy: Ba zan tattauna da Puigdemont ba | Labarai | DW | 22.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rajoy: Ba zan tattauna da Puigdemont ba

Firaministan Spain Mariano Rajoy ya yi watsi da bukatar jagoran 'yan aware na Kataloniya Carles Puigdemont na su sadu su tattaunawa.

A cikin wata hira da aka yi da shi, firaministan na Spain ya ce wadda ta kamata ya zauna ya tattauna da ita, ita ce Ines Arimadas shugabar wadanda ba su amince da yancin kan ba na Kataloniya. Yanzu haka dai Carles Puigdemont tsohon shugaban Kataloniyar na yin gudun hijira a Beljiyam.