Raila Odinga zai sake takara a zaben Kenya | Labarai | DW | 27.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Raila Odinga zai sake takara a zaben Kenya

Tsohon Firaministan kenya Raila Odinga zai sake kalubalantar Ohuru Kenyatta a zaben shugaban kasa da zai gudana cikin watanni hudu masu zuwa. kawancen jam'iyyun adawa ne suka tsayar da shi.

Gamayyar jam'iyyun adawa a Kenya ta sake tsayar da tsohon Firaminista Raila Odinga a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 8 ga watan Agusta mai zuwa na 2017. A yayin wani gangami da jam'iyyun na adawa suka shirya a birnin Nairobi ne Odinga mai shekaru 72 ya bayyana cewar shi ne aka amince da shi a matsayin wanda zai kalubalanci shugaba Uhuru Kenyata.

So uku ne dai Raila Odinga ya tsaya takarar shugabancin kasar Kenya ba tare da kwalliyarshi ta biya kudin sabulu ba. Ko da a zaben 2013 sai da aka dama da shi kafin ya sha kaye a hannun shugaba mai ci yanzu. 'Yan Kenya miliyan 19 ne suka cancanci kada kuri'a a zaben na gama gari wato na 'yan majalisa da na shugaban kasa da na gwamnoni da kuma na kananan hukumomi. Sai dai rikicin bayan zabe da ya barke shekaru 10 da suka gabata ya haddasa mutuwar mutane kimanin dubu da 100.