Rage wa'adin shugaban kasa a Laberiya | Labarai | DW | 16.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasar Laberiya

Rage wa'adin shugaban kasa a Laberiya

Galibin jama'ar Laberiya ta nuna goyon baya ga yunkurin Shugaba George Weah na rage wa'adin shekarun da shugaban kasa ya kamata ya yi a kan kujerar mulki.

Sakamakon da aka fara fitarwa na kuri'ar jin ra'ayin jama'a a kasar ne ya tabbatar da hakan. Nan da 'yan makonni masu zuwa ake sa ran samun kammalallen sakamakon zaben. Sai dai kuma a gefe guda wasu sun fara nuna damuwarsu kan kada Shugaba Weah ya yi amfani da gyaran tsarin mulkin ya shigo musu da wata dabara ta tsawaita zamansa kan kujerar shugabanci kamar yadda aka shaida hakan a wasu kasashen Afirka.

To amma wannan na zuwa ne a yayin da a bangaren sakamakon zaben Sanatoci da aka fitar, ya nuna cewa jam'iyyar ta George Weah ta sha kashi, inda cikin kujeru bakwai da aka fitar da sakamakon zabensu, jam'iyyar adawa ta samu kujeru hudu, yayin da jam'iyya mai mulki ke da kujeru biyu kawai. To sai dai akwai sauran kujeru takwas da ba a kai ga bayyana sakamakonsu ba.