Raɗaɗin Zafi – Canjin Yanayi | Learning by Ear | DW | 18.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Raɗaɗin Zafi – Canjin Yanayi

Afirka na fama da raɗaɗin zafi. Zafi sai ƙara ƙaruwa yake yi, lamarin dake haddasa fari, ambaliyar ruwa da ƙarancin abinci. Shin wane irin gudummawa zaka iya bayarwa akan haka?

default

Ko da yake ba laifinka ba ne, amma zaka yi fama da tasirinsa. Nahiyar Afirka ce zata fi fama da raɗaɗin canjin yanayi duk da cewar ƙasashen Turai da Amurka su ne suka fi fitar da hayaƙi mai guba ta carbon dioxide zuwa sararin samaniya – wannan hayaƙi na gas na ɗaya daga cikin uammal'aba'isin ɗimamar yanayin duniya.

Afirka zata fi fama da matsalar saboda galibi ta dogara ne akan noma. Sassa da dama na nahiyar tuni suka shiga ƙaƙa-nika-yi da matsaloli na fari da raɗaɗin zafi da ƙarancin ruwan sama ta yadda da wuya suke samun wata damina mai albarka.

Shin ta yaya zaka iya ba da haɗin kai ga mutanen dake fafutukar yaƙi da canjin yanayi a duk faɗin nahiyar kuma wani mataki zaka iya ɗauka a ƙauye ko garinku. Wannan shi ne abin da Carol da Lorna da Alex ke mayar da hankali kansa a wasan kwaikwayo na shirin Ji Ka Ƙaru akan canjin yanayi. Wasu matasa ne su huɗu suka tsayar da shawarar ɗaukar wani mataki bayan da suka samu labarin shirin kafa wata sabuwar tashar wutar lantarki a ƙauyensu. A cikin wannan zarafin suka gano mummunar illar canjin yanayi.


Sauti da bidiyo akan labarin