1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pompeo: Za mu cigaba da goyon bayan Isra'ila

Zulaiha Abubakar
April 29, 2018

Sakataren tsaron kasar Amirka Mike Pompeo ya jaddada kudirin kasar na cigaba da ba kasar Isra'ila goyon baya yayin da ya ke ganawa da Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu a yau Lahadi a ziyarar da ya kai kasar.

https://p.dw.com/p/2wsZz
Mike Pompeo da Benjamin Netanyahu
Mike Pompeo da Benjamin NetanyahuHoto: picture-alliance/AA/GPO/H. Zach

Sakatarn na harkokin wajen Amirka ya kuma kara da bayyana matukar damuwar Amirka kan irin barazanar da kasar Iran ke cigaba da yi wa Isra'ila da kuma yunkurin mallakar yankin Gabas ta Tsakiya da kasashen biyu su ke zargin Iran din da yi, daga nan sai ya kara da cewar Amirka a shirye ta ke don janyewa daga batun yarjejeniyar makamai masu linzami da Iran in dai ba a cimma daidaito ba. Tun da fari Firaminista Natanyahu wanda ya shaidawa manema labarai cewar ganawar ta su z ata maida hankali ne a kan Iran ya bayyana Mike Pompeo a matsayin masoyin Isra'ila.