Pistorius ya kalubalanci daukaka kara | Labarai | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pistorius ya kalubalanci daukaka kara

Masu shigar da kara a Afirka ta Kudu sun daukaka kara dangane da hukuncin da aka yanke wa Oscar Pistorius

Lauyoyin Oscar Pistorius, shahararren dan tseren masakun nan sun kalubalanci daukaka karar da masu shigar da kara suka yi dangane da hukuncin da aka yanke masa bayan da aka same shi da laifin kisa amma ba da gangan ba.

A watan Disemban bara ne kotun ta baiwa masu shigar da karar izinin daukaka kara bayan da aka yanke mi shi hukunci mai sassauci bayan ya kashe budurwarsa. Su dai masu kare Pistorius sun ce an yanke hukuncin ne bisa hujjojin da aka gabatar a kotu, ba bisa la'akari da yadda ake fassara doka ba, kuma dan haka, ba zasu iya daukaka kara ba.

A yanzu haka dai za a fara sauraron karar daga ranar 13 ga watan Maris mai zuwa, idan Allah ya kai mu. A yanzu haka dai Pistorius, na wa'adinsa a asibitin kurkuku, nesa da gidajen yarin yan Afirka ta Kudu da ke ciki da suka yi kaurin suna wajen ajiye masu laifin da suka yi fice wajen ta'addanci a kungiyance