Oscar Pistorious fitattacen dan tseren nakasassu ne na Afirka ta Kudu wanda ya samu nasarori na lashe gasa iri-iri da aka sanya.
Tun ya na dan shekaru 17 ne ya fara shiga gasar nakasassu kuma a cikin shekarar 2012 ya shiga gasar Olympics ta sauran mutane wadda aka yi a birnin London na Burtaniya. A cikin shekarar 2013 ne aka haramta masa yin tsere biyo bayan harbe budurwarsa da ya yi, wato Reeva Steenkamp.