Paul Wolfowitz ya shiga tsaka mai wuya | Labarai | DW | 20.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paul Wolfowitz ya shiga tsaka mai wuya

Ana cigaba da yiwa shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz matsi lamba, bayan tattaunawa da kwamitin zartaswa na cibiyar kudin ya gudanar a yanmacin jiya alhamis, inda ya amince akan nagartattun matakai da za’a dauka domin tunkarar duk banbance banbance daka taso a game da tabargazar da ake zarginsa da aikatawa.

Wolfowitz na fuskanatar matsin lamba daga ma’aikatan bankin akan ya yi murabus, a game da irin rawar da ya taka wajen karawa wata ma’aikaciyar bankin, kuma budurwar sa albashi. Ko da yake Wolfowitz ya aiwatar da wadan su muhinman canje canje a wasu bangarori na shugabancin bankin, amma yaki ya yi murabus kamar yadda suka nema.