1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma yayi wa 'yan gudun hijira addu'o'i a Lampedusa

Mohammad AwalJuly 8, 2013

A ziyarar da ya kai a tsibirin dake a kasar Italiya, Paparoma Francis ya kuma ajiye furanni don tunawa da daruruwan 'yan gudun hijira da suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/193rI
Poep Francis 'C) waves to faithful as he arrives to lead a mass during his visit to the island of Lampedusa, a key destination of tens of thousands of would-be immigrants from Africa, on July 8, 2013. Pope Francis called for an end to 'indifference' to the plight of refugees on Monday on a visit to an Italian island where tens of thousands of migrants from Africa and the Middle East first reach Europe. AFP PHOTO / MARCELLO PATERNOSTRO (Photo credit should read MARCELLO PATERNOSTRO/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Paparoma Francis yayi addu'o'in tunawa da 'yan gudun hijira da suka rasa rayukansu a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya dake tekun Bahar Rum. Daga cikin wani kwale-kwale Paparoman ya ajiye furanni cikin tekun don tunawa da dinbim 'yan gudun hijira da suka rasa rayukansu lokacin da suke kokarin tsallake tekun daga arewacin Afirka. A wani bikin addu'o'i da ya jagoranta a wani filin Allah Ta-ala, shugaban na mabiya darikar Katholika a duniya yayi suka ga yadda ake fatali da mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar ke ciki. A lokaci daya kuma yayi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kula da 'yan gudun hijirar. Kimanin sa'o'i biyu gabanin isar Paparoma Francis a tsibirin na Lampedusa, wani karamin jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira kimanin 166 ya isa yankin. Bakin haure da kuma 'yan gudun hijira kimanin 4000 daga arewacin Afirka suka shiga Lampedusa a watanni shidan farko na wannan shekara ta 2013.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe