Paparoma ya shawarci matasa su rungumi adalci | Siyasa | DW | 25.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Paparoma ya shawarci matasa su rungumi adalci

Paparoma Francis ya yi ya wannan kira ne a jawabinsa ga dubban daruruwan matasa 'yan darikar Roman Katolika a Brazil, a bangaren ranar bukin matasa ta duniya.

Wannan dai na bangaren rangadin farko da Paparoman wanda dan asalin yan latin Amurka ne ya ke yi bayan hawansa kujerar shugabancin darikar.

Wannan shine irin taryan da dubban daruruwan matasan suka yi wa jagoran Roman katolika na Duniya. A yayin wannan rangadi a yankinsa na asali dai, Paparoma Francis ya gargadi kasashen yankin latin Amurka da su guji halalta Miyagun Kwayoyi, tare da nunar da cewar kalaman sassaucin ra'ayin na siyasa ba zai rage wannan matsala ba. Ya yi kira ga 'yan Roman Katolikan da su guji son abun duniya, inda ya gana da 'yan kwaya tare da yi musu, tare da yin suka ga dillan wadanda ke dada ruruta halin da suke ciki.

A kasar ta Brazil dai Paparoma Francis ya ziyarci daya daga cikin muhimman wuraren bauta da ke yankin latin Amurka da ake kira "Our lady of Aparecida" inda ya yi masa lakabi da wurin shan wahalar bil'adama-wanda ke zama asibi ne a birnin Rio inda ake kula da kuma jinyar masu shan kwaya.

Tun Paparoma yana matashin dai ya sha nunar da bukatar ayi watsi da kwadayin kudi da mulki, tare da jaddada bukatar chucinan Katolik su mayar da hankali wajen taimakawa talakawa da wadanda al'umma ta yi watsi da su.

Dubban daruruwan 'yan darikar ce dai suka taryi Paparoma Francis a harabar wurin bautan na "Our lady of Aparecida", wanda ke wata gunduwa da ke tsakanin Rio da Sao Paola.

Duk da sanyi saboda ruwan sama da ya sauka, 'yan braziliyan sun yi dafifi domin ganin Paparoma a wannan ziyara da ya kai a wannan wurin bauta dake da muhimmanci ga nahiyar da ma wa shi kansa Francis; " ni ma na zo domin kwankwasa kofar gidan Mary, wadda ta girmar da Yesu cikin kauna, domin ta taimaka mana dukkanmu, Pastoci, Iyaye da kwararru, wajen ilimantar da matasa dabi'u masu kyau, wanda zai taimaka musu gina kasa da ma duniya mai adalci da hadin kai".

Paparoma Francis dai ya kai ziyara zuwa unguwar marasa galihu da ke birnin Rio de Janeiro, yankin da ya fuskanci tashin hankali a shekarun baya wanda har yasa ake kiran wurin "zirin gaza".Duk da tsauraran matakan tsaro da tsananin sanyi saboda ruwan sama dake zuba, Francis ya yi ta kutsawa tsakanin taron jama'a ba tare da lema ba. Inda ya yi ta sunbatar matasa da tsofaffi yana sa musu albarka, kafin ya shige zuwa majami'ar da ke yankin. Inda sawa sabon Bagadi na majami'ar.

Motarsa mai budadden kai dai a yawancin lokuta yana tafiya ne shi kadai, kasancewar Paparoma ya fi tafiya da kafa tsakanin wadannan al'umma da kafa yana sa musu albarka, inda kowa ya ke muradin mika masa kyauta.

Jagoran Roman katolikan ya jaddada bukatar matasa su taka rawar gani wajen yaki da cin hanci da rashawa a daidai lokacin da kasar ta Brazil ke fuskantar boren kasa baki daya. Sa'annan ya shawarci gwamnati da ta sauya salon kulawa da unguwannan matalauta, idan har tana muradin yaki da talauci.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin