Paparoma Francis ya kalubalanci ′yan siyasa | Labarai | DW | 21.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis ya kalubalanci 'yan siyasa

Shugaban darikar katolika ya bukaci hamshakai su yi kasuwanci da zai sa mai karamin karfi ya amfana ta yadda za a daina lalata muhalli a duniya.

A jawabinsa Paparoma Francis ya fadawa shugabannin tattalin arziki da 'yan boko da 'yan siyasa a duniya cewa, su duba irin rawar da suka taka wanda ya yi sanadin talauci a duniya.

A sakonsa da aka karanta a taron tattalin arziki da aka bude jiya Laraba a Davos, Paparoman ya yi kira da a kawo sauyi ta yadda kasuwanci zai yi adalci ga matalauci da hamshaki, kana ya kare mahalli.

Shugaban darikar Katolikan ya kuma ja kunnen shugabannin, da su yi hankali kan kere-kere da fasahohin zamani, domin kada su ce za su maye gurbin ayyukan bil Adama mai rai ke yi, da wata na'urara ko mutum-mutumi.