Paparoma Francis na ziyara a Sweden | Labarai | DW | 31.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis na ziyara a Sweden

Paparoma Francis ya isa a birnin Malmo na Sweden domin halatar bukukuwan zagayowar cikar shekaru 500 da bulo da bangaran mabiya darikar Protestant.

Manufar wannan ziyara ta Paparoma shi ne na kara kusantar da mabiya darikar Katolika da 'yan uwansu na Protestant wanda aka kwashe sama da shekaru 50 ana tattaunawa tsakanin darikun biyu na Kirista domin samun fahimtar juna,bayan da a shekara ta 1517 wani limannin Cocin Katolikan Martin Luther ya kawo sauye-sauye a game da addinin na Kirista na mabiya darikar Roman Katolika.Cocin na Protestant na Holland sun ba da izinin na jagorancin mata a Cocina tun a shekara ta1960, kana sun halarta auren jinsi tsakanin maza da maza ko mata da mata.