1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paolo Rossi ya mutu sakamakon jinya da ya sha

December 10, 2020

Shahararren tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Italiya Paolo Rossi ya rigamu gidan gaskiya.

https://p.dw.com/p/3mX4F
Italien Paolo Rossi 1982
Hoto: AP Photo/picture alliance

Shahararren tsohon dan wasan kwallon kafar nan na kasar Italiya Paolo Rossi, ya mutu ya na da shekaru sittin da hudu a duniya. Rashin na mamacin na zuwa ne kasa da wata guda da mutuwar Diego Maradona, shi ma wani dan wasan ta kwallon kafa da ya shahara.

Wata kafar gidan talabijin din kasar ta Italiya ta ruwaito cewa, Rossi ya mutu ne sakamakon wata rashin lafiya da aka gagara shawo kanta.

Mamacin dai ya taba lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 1982 inda Italiyar ta lallasa kasar Brazil gabanin ta dauki kofin wanda Rossin ya ci kwallaye uku a wasan.