Palesdinawa 500 ne suka mutu a zirin Gaza | Labarai | DW | 21.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Palesdinawa 500 ne suka mutu a zirin Gaza

Rikici tsakanin Izra'ila da kuma Hamas na ruruwa inda ake samun karuwar mace-macen Palestinawa sakamakon ruwan bama-baman da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.

Akalla Palestinawa 502 ne suka rasu tun bayan barkewar rikin Izra'ila da Hamas. Fiye da 140 daga cikinsu dai an kashesu ne a jiya Lahadi (20.07.2014). A garin Chajaya wani kauye dake gabacin birnin Gaza, ruwan bama-baman da sojojin Izra'ila suka yi, ya yi sanadiyar rasuwar akalla Palestinawa 72 a jiya lahadi a cewar wata majiya ta ma'aikatan agaji.

A bangaren Izra'ila kuwa, an kashe sojoji 13 a cikin 'yan sa'o'i 24 na baya-bayannan, wanda ya kai adadin sojoji 18 na Izra'ila da suka rasu tun bayan soma wannan rikici.

A wannan Litinin ma dai, an kashe Falestinawa 9 a garin Rafah dake kudancin Gaza, bakwai daga cikinsu yara kanana ne kuma 'yan gida guda.

Cikin wata sanarwa da ta fitar , rundunar sojen Hamas ta ce dakarunta sun kutsa har cikin Izra'ila, inda suka ragargaza wata mota mai dauke da sojojin na Izra'ila. Sannan kuma a halin 'yanzu suna ci gaba da fafatawa da abokan gaba.

kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwarsa inda ya yi kira da a dakatar da wannan rikicin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe