Palasdinu: Kungiyar PLO ta yi watsi da Isra′ila | Labarai | DW | 16.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Palasdinu: Kungiyar PLO ta yi watsi da Isra'ila

A kasar Palasdinu kwamitin gudanarwa na kungiyar kwatar 'yancin kasar Palasdinu wato OLP ya dauki mataki dakatar da amincewa da kasantuwar Isra'ila a matsayin kasa.

A kasar Palasdinu kwamitin gudanarwa na kungiyar kwatar 'yancin lasar Palasdinu wato PLO ya dauki mataki dakatar da amincewa da kasantuwar kasar Isra'ila a matsayin kasa, matakin ke a matsayin babban tuballin da aka kafa shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawan. 

Kwamitin gudanarwa na Kungiyar ta PLO ya kada kuri'ar dawowa daga matakin amincewa da Isra'ila a matsayin kasa bayan wani taron kwanamki biyu da ya gudanar a birnin Ramalla na yammacin kogin Jodan a karkashin jagorancin shugaban Palasdinawan Mahmud Abbas. Wannan mataki na kungiyar PLO na a matsayin martani ga matakin da shugaba Trump na Amirka ya dauka a ranar shida ga watan Disambar da ya gabata na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.