1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a siyasar Pakistan

Abdullahi Tanko Bala
May 24, 2023

Gwamnatin Pakistan na nazarin haramta jam'iyyar tsohon Firaministan kasar Imran Khan bayan shafe kwanaki ana fama da tashin hankali

https://p.dw.com/p/4Rlul
Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
Hoto: K. M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Karuwar tashe tashen hankula sun biyo bayan kama Imran Khan da hukumomi suka yi a farkon watan Mayu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Ministan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ya baiyana wa 'yan jarida cewa tuni gwamnatin ta fara nazari kan wannan mataki saboda barazanar da jam'iyyar ke yi ga dorewar kasar wanda kuma ba za a lamunta da shi ba.

Shi dai tsohon Firaministan Imran Khan yana takun saka da gwamnatin Pakistan da kuma sojoji da suka mulki kasar kai tsaye ko kuma suka jagoranci gwamnatocin fara hula ta hanyar sa ido kan ayyukan su.