Akalla mutane tara ne suka mutu a wani turmutsitsin da ya barke a birnin Karachi da ke kudancin Pakistan,yayin da jama'a suka garzaya zuwa wata masana'anta da aka shirya rabon sadaka na azumin Ramadan.
Turmutsitsin ya faru ne a lokacin da mata mabukata da ‘ya'yansu suka cincirindo a masanantar.inda cinkosso jama'a ya yi yawa.Yanhzu haka an kai gawarwakin mata shida da yara uku zuwa asibiti in ji kakakin 'yan sanda birnin na karashi Muhammad Farukh.