1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Jana'izar mamatan gobarar jirgin kasa

Gazali Abdou Tasawa
November 1, 2019

A wannan Juma'ar kasar Pakistan ta soma jana'izar mutanen da suka mutu a hadarin gobarar jirgin kasa na fasinja a jihar Pendjab da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/3SKAK
Pakistan Zugunglück
Hoto: picture-alliance/AA/M. Bilal

A kasar Pakistan an soma gudanar da jana'izar mutanen da suka mutu a wani hadarin gobarar da ta tashi a wani jirgin kasan fasinja a ranar Alhamis a Jihar Pendjab a sakamakon fashewar wata tukunyar gaz, lamarin da ya yi sanadiyyar mutane akalla 74 wasu da dama kuma suka jikkata.

Iyalai, dangi da 'yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su sun shafe dare a ofishin 'yan sanda na birnin inda ake karbar gawargwakin mutanen da kuma mika wa iyalan takardar tabbacin mutuwar a hakumance.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance gawarwakin mutane da dama da gobarar ta kone ba, har sai an gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA wanda ke daukar akalla makonni hudu. A safiyar Alhamis ne dai gobarar ta tashi a cikin wasu taragan jirgin kasan dauke da matafiya zuwa wani bikin addini na shekara-shekara a birnin Raiwind kusa da birnin Lahore.