Pakistan na ci gaba da fuskantar hare -hare | Labarai | DW | 28.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan na ci gaba da fuskantar hare -hare

Ana ci -gaba da fuskantar hare-haren bom a kasar Pakistan kafin gudanar da zabe a ranar 11 ga watan Mayu

Sa'o'i kalilan bayan hare-haren da aka fuskanta a birinin Karachi da ke yankin arewa maso yammacin kasar, an kuma kai wa ofishin wata jam'iyya hari. Sanarwar da aka bayar a hukumance ta yi nuni da mutuwar mutane hudu a baya ga mutane 20 da suka samu raunuka a cikin harin da aka kai akan ofishin wani dan takara a gundumar Kohat da ke lardin Khyber-Pakhtunkhwa. An kuma samu mutuwar mutane uku a cikin wani hari da aka kai akan ofishin wani dan takara mai zaman kansa a wata unguwa da ke wajen lardin Pashewar. Wasu kuma da dama sun samu raunuka. Mutane hudu ne dai suka mutu a cikin harin da ya auku a birnin Karachi , Wasu kuma su 55 sun samu raunuka. Ofishin jam'iyyar Muttahida Qaumi Movement aka nufaci da wannan hari.

Ita dai jam'iyyar Muttahida Qaumi tuni ta rufe ofisoshinta a sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa akan ofisoshin jamiyu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh