1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khan zai ci gaba da zanga-zanga a Pakistan

November 26, 2022

Tsohon firaministan da ya 'yan majalisar Pakistan suka tsige a watan Afrilun da ya gabata, a wannan Asabar, ya ce zai ci gaba da yekuwar gudanar da zabe a kasar ko da kuwa hakan zai zama ajalinsa.

https://p.dw.com/p/4K8SY
Pakistan I Imran Khans - Islamabad
Hoto: W.K. Yousafzai/AP/picture alliance

Tsohon firaministan Pakistan Imran Khan ya lashi takobin ci gaba da matsa wa gwamnatin kasar lamba ta shirya zabe kafin watan Oktoba mai zuwa lokacin da wa'adin majalisar dokokin kasar zai kare.

Khan ya sha wannan alwashi ne a yayin jawabinsa na farko ga magoya bayansa tun bayan harbin da aka yi masa a wani yunkuri da yace an shirya domin yi masa kisan gilla a farkon wannan watan.

Khan dai ya zargi firaminista mai ci Shehbaz Sharif da ministan kula da harkokin cikin gida da wasu manyan sojoji a matsayin wadanda suka kitsa harbin da dan bindiga ya yi masa. To amma tuni suka musanta wannan zargi.