1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bom ya tarwatse a cikin kasuwar Pakistan

January 20, 2022

Wani sabon gungun 'yan aware da ke a lardin Balochistan na kasar ta Pakistan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa shi ne ya kai wannan mummunan hari.

https://p.dw.com/p/45q8L
Pakistan | Anschlag in Lahore
Hoto: K.M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Wani bom da ya tarwatse a cikin wata babbar kasuwa a gabashin Pakistan ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da jikkata mutane sama da 20. 'Yan sanda sun ce lamarin ya faru a wannan Alhamis  bayan da mahara suka tayar da bom din da suka dana a jikin wani mashin da suka ajiye a tsakiyar kasuwar mai cike da  jama'a. 

A cikin 'yan watannin nan, gungun  'yan awaren da ya kai harin ya rika kai hare-hare jefi-jefi domin tilasta wa hukumomi sanya sa cikin wadanda za a rika raba arzikin ma'adanan yankin da su.