1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Arangama da magoya bayan Khan

Abdullahi Tanko Bala
March 15, 2023

Magoya bayan tsohon firaministan Pakistan Imran Khan sun yi arangama da 'yan sanda a mahaifarsa Lahore. Hukumomi sun yi kokarin kama Khan wanda ke fuskatar shari'a a gaban kotu.

https://p.dw.com/p/4OiV5
Pakistan | Zusammenstöße von Unterstützern von ex-PM Khan und der Polizei
Hoto: Arif Ali/AFP

Mutane da dama sun sami raunuka yayin artabu tsakanin magoya bayan tsohon firaministan da jami'an 'yan sanda a kofar gidansa a Lahore. Lamarin ya faru ne a lokacin da 'yan sanda suka yi kokarin kama Khan kwana guda bayan da ya ki baiyana a gaban kotu.

Magoya bayan tsohon firaministan sun rika jifar da duwatsu yayin da 'yan sanda suka mayar da martani da harba hayaki mai sa hawaye suka kuma yi wa gidan kawanya.

Kotun ta aika wa Khan sammaci ya gurfana a gabanta kan zargin sayar da kyaututtuka na kasa da aka bayar lokacin da yake kan karagar mulki.