Pakistan: An dakatar da aikin wasu kungiyoyi | Labarai | DW | 22.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan: An dakatar da aikin wasu kungiyoyi

Hukukumoi a Pakistan sun takaita aikin kungiyoyin masu zaman kansu, yayin da wasu ma aka dakatar da su.

Kimanin kungiyoyi masu zaman kansu 27 ne ofishin ministan cikin gida ya tsaida aiknsu wadanda kuma aka bai wa watannin uku kacal su dakatar da aiki. Daga cikin kungiyoyin da aka dakatar har da World Vision da OXFAM. Ministan cikin gidan na Pakistan Talal Chaudhry ya ce yawancin kungiyoyin ba su kan kaida.