Pakistan: Abbasi ya zama Firaminista | Labarai | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan: Abbasi ya zama Firaminista

Majalisar dokokin Pakistan ta zabi Khaqan Abbasi a matsayin sabon firaministan kasar wanda zai canji Nawaz Sharif da kotun kolin kasar ta tsige daga mukaminsa.

Pakistan Islamabad - Shahid Khaqan Abbasi (picture-alliance/AP Photo/A. Naveed)

Shahid Khaqan Abbasi sabon Firaministan kasar Pakistan.

Rahotannin daga Islamad babban birnin kasar Pakistan na cewa, a wannan Talatan ce aka zabi tsohon dan kasuwar nan Shahid Khaqan Abbasi a matsayin sabon firaministan kasar ta Pakistan yayin wani zabe da aka yi a majalisar dokokin kasar wanda shi ne zai canji Nawaz Sharif, da kotun kolin kasar ta tsige shi daga mukaminsa. Shugaban majalisar dokokin ta Pakistan ne dai Sardar Ayaz Sadiq ya tabbatar da wannan labari.

Shi dai Abbasi wanda daman ake kallo a matsayin wanda zai iya lashe zaben ganin yadda ya amu goyon bayan hambararran Firaministan Sharif, da kuma jam'iyyarsa ta PML-N da ke da rinjaye a majalisa, ya samu kuri'u 221 fiye da adadin 172 da ake nema domin samun mukamin na Firaminista.