Osinbajo ya sa hannu a kasafin kudin bana | Labarai | DW | 12.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Osinbajo ya sa hannu a kasafin kudin bana

Bayan share tsawon lokaci ana zaman jira da yammacin Litinin ne shugaban Tarayyar Najeriya da ke zaman riko farfesa Yemi Osinbajo ya rattaba hannu kan kasafi na triliyan bakwai da miliyan dubu dari hudu

Ana fatan kasafin kudin na bana zai kafa dan ba na ficewar kasar cikin halin kunci sannan da sake dora ta a bisa hanya ta cigaba na tattali na arziki. To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai batu na korafin ya fara fitowa daga bangaren zartarwar da duk da sa hannun ke neman jeri na sauye sauye a cikin kasafin. Sabon kasafin dai na zaman irinsa mafi dadewa da yan kasar sukai zaman jira kamun iya kaiwa ga fara aiwatar dashi.

Wasu sun dora alhakin jinkirin bisa rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Birtaniya. Najeriya dai ta fada cikin mummunan matsalar tattalin arziki, ko da yake a yanzu ta dan fara farfadowa, don haka ake ganin sa hannu bisa kasafin kudin, zai iya karfafa gwiwar kamfanoni da 'yan kasuwa.