OPCW. An yi anfani da makami mai guba a Siriya | Labarai | DW | 13.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

OPCW. An yi anfani da makami mai guba a Siriya

Hukumar da ke yaki da makamai masu guba OPCW ta ce an yi anfani da sinadarin Chlorine da Sarin kan jama'a da ke rayuwa a karkashin ikon 'yan tawaye a birnin Hama na Siriya.

Hukumar ta ci gaba da cewa an yi anfani da Sarin a birnin Ltamenah a yankin Hama a ranar ashirin da hudu da ashirin da biyar na watan Maris a shekarar 2017 a yankin na Hama da ke kudancin kasar. An tabbatar da hakan ne bayan binciken hukumar.

Wadannan sinadaran na daga cikin wadanda aka haramta yin anfani da su ko da a lokacin rigingimu ne. An zargi bangaren gwamnatin Bashar al-Assad da laifin yin anfani da makaman masu guba a kan al'umma a yankin da a wancan lokacin ke karkashin ikon 'yan tawaye, lamarin ya janyo asarar rayukan mutane barkatai.